Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Dage Sauraron Shari'ar Kanu Zuwa Watan Fabrairu 


Nnamdi Kanu da lauyoyinsa a zaman kotun da aka yi a ranar Alhams (Channels TV)
Nnamdi Kanu da lauyoyinsa a zaman kotun da aka yi a ranar Alhams (Channels TV)

Babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja a Najeriya ta dage zaman shari'ar Nnamdi Kanu shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu.

An dage zaman kotun zuwa watan Fabrairu ne bayan kin amsa sabbin tuhume-tuhume takwas da gwamnatin tarayyar Najeriya ke masa masu alaka da ta'addanci da cin amanar kasa, kari kenan a kan guda bakwai na baya.

Nnamdi Kanu, wanda aka shigo da shi cikin kotun da misalin karfe 10:15 na safe, ya ce bai aikata wani laifi ba a dukkan zarge-zargen da gwamnatin Najeriya ke yi masa ya na mai cewa sabbin zarge-zargen da aka kara na kama da na baya, inda ya dage da cewa sai kotu ta saurari bukatarsa ta farko inda ya kalubalanci cancantar tuhumar da ake masa.

A nasa bangaren, jagoran lauyoyin shugaban kungiyar IPOB, Mike Ozekhome, ya bayyana yakinin cewa idan kotu ta yi nazari mai zurfi kan zarge-zargen da ake yi wa Kanu, zata bada belin shi ba tare da wasu sharudda ba.

Bayan da Kanuya ki amsa laifukan da ake tuhumarsa da su da kuma neman a saurari bukatarsa ta farko ta kalubalantar cancantar tuhumar da ake masa, lauyan masu shigar da kara Labaran Magaji, ya shaida wa kotun cewa a shirye yake ya ci gaba da shari’ar, ya kuma kara da cewa ya kawo shaidu biyu da za su ba da shaida kan wanda ake tuhuma.

Haka kuma lauyan na gwamnati Labaran Magaji, ya bayyana mamaki kan yadda Kanu ya nesanta kansa da batun shi mamba ne a kungiyar IPOB bayan karanta daya daga cikin tuhumar da ake masa ta zama jagoran kungiyar.

Kotun, a karkashin jagorancin mai shari’a Binta Nyako ta amince a saurari bukatun da ke gabanta a game da cancantar tuhumar Kanu inda ta dage shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:

Kotu Ta Dage Sauraron Shari'ar Kanu Zuwa Watan Fabrairu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00


XS
SM
MD
LG