Sojojin Nigeria Sun Kaddamar Da Bikin Share Gudunbali A jihar Borno

Sojoji sun share Gudunbali

Babban hafsan sojojin Najeriya ya jagoranci bikin share gari da sojoji keyi kowace shekara a garin Gudunbali da sojoji suka kwato daga kungiyar Boko Haram.

Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai ya kaddamar da sharar gona daga cikin garin Gudunbali da sojoji suka kwace daga yan Boko Haram.

Janar Buratai ya ce sun kaddamar da share garin ne domin tabbatarwa mutanen garin cewa sojoji sun ci karfin ‘yan Boko Haram a yankin kuma rundunarsu za ta ci gaba da basu kariya.

Tun a ranar 18 ga watan Nuwambar shekarar 2015 sukakwato garin bayan wani mugun gumurzu da suka yi da ‘yan Boko Haram da ya lakume rayukan sojoji da dama.

Janar Buratai yace, Gudunbali sanannen gari ne da aka sanshi da harkokin kasuwanci da zaman lafiya kafin ‘yan Boko Haram su tarwatsashi. Janar Buratai ya ce sun zabi Gudunbali ne su kaddamar da bikin a matsayin gwaji saboda su ci gaba da kara kaimi a yakin su da Boko Haram a shiyar arewa maso gabashin Najeriya. Baicin hakan sun zabi garin ne don yadda ake gudanar da harkokin kasuwanci. Garin na da mahimmancin gaske saboda yana kusa da garin Baga da yankin tafkin Chadi da ma kasar baki daya.

Janar Buratai ya nuna farin cikinsu kasancewa wadanda suka bar garin kimanin shekaru bakwai da suka gabata sun dawo tare da wasu suna ci gaba da rayuwarsu kamar yadda su keyi a can baya.

A saurari rahoton Haruna Dauda Biu domin jin karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Najeriya Sun Kaddamar Da Bikin Share Gudunbali da Suka Kwato Daga Boko Haram – 3’ 51”