Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijirar Guzamala Sun Fara Komawa Gida


'Yan gudun hijiran a yayin da ake jigilarsu zuwa garinsu
'Yan gudun hijiran a yayin da ake jigilarsu zuwa garinsu

A yau Talata ne ‘yan gudun hijirar Guzamala da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi a garin Maiduguri suka fara komawa garin su na asali a karamar hukumar Guzamala da ke Jihar Borno

A wata sanarwar da jami'i mai hulda da jama'a na rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Texas Chukwu ya fitar, 'yan gudun hijirar da adadinsu ya kai kimanin 2,043 ne suka fara komawa garin su na asali, kuma sun kasance wadanda suka fara nuna sha’awarsu ta komawa mazauninsu na asali domin ci gaba da sana’oinsu na noma da kamun kifi da kuma sauran harkokinsu na yau da kullum.

A lokacin da yake jawabi yayin da aka kaddamar da kwashe daga sansanin ‘yan gudun hijirar na Bakassi, kwamandan Operation Lafiya Dole Manjo Janar Rogers Nicolas ya bayyana cewa babban abin da babban hafsan sojojin kasa wato Janar Yusuf Buratai ya sa a gaba yanzu shine ya tabbatar da cewa ‘yan gudun hijirar da ke son komawa gida sun ci gaba da rayuwarsu kamar yadda ta ke a baya kuma a cikin kwanciyar hankali.

Ya kara da cewa shawarwarin da aka yi na maidasu gida sun hada da jami’an sojoji da gwamnatin Jihar Borno da kuma Jami’an karamar hukumar Guzamala baki daya, inda ya ce sojoji sun kara tsaurara matakan tsaro a yankin. Haka kuma an gudanar da sharar daji domin manoma su ci gaba da shuka a gonakin su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG