Sojojin Sudan, Kungiyoyin 'Yan Adawa Sun Amince a Raba Mumakai

Wannan ci gaba da aka samu, matakai ne da za su yi sharar fage wajen mika muki a kasar ta sudan, wacceta kwashe watanni tana fama da rikice-rikice, tun bayan da sojoji suka hambarar da dadadden shugaban kasar, Omar al-Bashir.

Wakilan gwamnatin mulkin sojin Sudan da gamayyar kungiyoyin da ke kare mulkin Dimokradiyya, sun rattaba hannu kan wata matsaya ta siyasa da aka cimma a yau Laraba, a matsayin wata yarjejeniya da za ta ba da dama a raba mukamai.

Ana sa ran za a sanya hannu a wani bangare na yarjejeniyar, ta tsarin mulki, a ranar Juma'a mai zuwa.

Wannan ci gaba da aka samu, matakai ne da za su yi sharar fage wajen mika muki a kasar ta sudan, wacceta kwashe watanni tana fama da rikice-rikice, tun bayan da sojoji suka hambarar da dadadden shugaban kasar, Omar al-Bashir.

Wannan yarjejeniyar ta raba makaman, ta ƙunshi kafa wata majalissa ta haddin gwiwa wacec aka dora mata alhakin shugabancin kasar har na kusan tsawon shekaru uku kafin a yi zabe.