SOKOTO: Mutane 7 Sun Mutu Sanidiyar Cin Wani Abinci

Abinci

Al'ummar garin Kaurar Yabo a karamar hukumar Yabo sun wayi garin safiyar yau talata cikin alhinin rasuwar mutane bakwai ‘yan dangi daya sanadiyar wani abinci da suka ci.

A hirar shi da Muryar Amurka, magajin gidan da abin ya faru, Mallam Umaru kauran Yabo ya bayyana cewa, da dare maidakin ta yi wani dambu na masara da kowa ya ci duk da wandanda ba gidan su ke ba, kuma ba a sami wata matsala ba.

Bisa ga cewsarsa, kafin su kwanta, mai dakin ta dauki sauran tsakin da ya rage ta baza a waje domin ya sha iska ba tare da ta rufe ba, kashe gari ta dauki tsakin ta kara da dambun da ya rage ta sake gyarawa ta ba yara su ka ci. Cin wannan dambun da safe ya yi sanadin mutuwar su.

Maigidan ya bayyana cewa, ba za su tantance aininin abinda ya yi sanadin mutuwar mutanen ba, ko daga tsakin ne ko kuma sauran dambun. Sai dai yace, sun kai mutanen da kuma sauran abinci asibiti domin a gudanar da bincike bayan da lamarin ya faru, sai dai a daidai lokacin dauko rahoton ya ce hankali ya koma kan rashin da su ka yi ba binciken sanadin ba.

Bisa ga bayaninsa, mutanen bakwai da suka rasu sun hada da matan aure biyu da kananan yara biyar. Maza uku mata hudu.

Kayan Marmari Abinci

A lokacin hada rahoton, jama'a suna ta tururwa zuwa gidan domin yin ta'aziya ga iyalan, ciki har da shugaban karamar hukumar Yabo Haliru Abubakar Kilgori wanda ya bayyana takaicin afkuwar lamarin da ya ce ya zama ishara ga kowa. Bisa ga cewarshi, tilas ne ganin abinda ya faru a dauki matakin ganin an rufe abinci da abinsha a ko yaushe

Wannan lamarin dai ba shine irinsa na farko da aka samu a Najeriya ba, domin ko a Sakkwato an samu haka a karamar hukumar Isa, kuma ba da jimawa ba an samu irin haka a jihar Zamfara.

Ko aranar Lahadin wannan makon, wadansu shida sun mutu a garin Enugu bayan sun dawo bukin aure, da suka hada da angon, yayinda aka kwantar da wadansu takwas a asibiti bayan da aka same su sun suma. Tuni rundunar 'yan sandan jihar Enugu ta kaddamar da bincike.

Masu sharhi akan lamurran yau da kullum na ganin akwai bukatar a dage wajen fadakar da jama'a akan yadda zasu kare kai daga irin wadannan musifu musamman mazauna yankunan karkara.

Abinci

A bayaninsa, farfesa Tukur Muhammad ya bayyana cewa, kamata ya yi jami'an kiwon lafiya da hukumomi su rika fadakar da jama'a a kai a kai game da irin wadannan abubuwa kasancewa ba wannan bane karon farko da haka ta faru tsakanin al'ummma.

Masu lura da al'amurra na ganin akwai bukatar mahukunta su kara zare damtse wajen sauke nauyin da ke kansu na kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Ku Duba Wannan Ma Hauhawar Farashin Kayayyaki A Najeriya Yafi Na Shekaru 17 Baya Muni

Saurari cikakken rahoton Mohammed Nasir cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

SOKOTO: Mutane 7 Sun Mutu Sanidiyar Cin Wani Abinci