Sudan Na Bikin Samar Da Yarjejeniyar Siyasa a Kasar

Cikin 'yan buki, harda duban dubatan mutane daga Atbara, wanda shi ne birni na farko da ya fara zanga-zangar neman hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al Bashir.

Kwamitin Rundunar Sojin wucin gadi na Sudan da jam’iyyun adawa sun sanya hannu kan wata yarjejeniya a karshen mako bayan zanga-zangar da aka shafe watanni ana yi. Koda yake da yawa daga cikin masu zanga-zangar suna dan shakkar sasantawar da aka yi a yarjejeniyar, an yi ta bukukuwa a birnin bayan sa hanu a yarjejeniyar.

Sa hannu kan yarjejeniyar siyasa ta Sudan a karshen mako ta hadu da kida, da raira-raire.

A cewar wani 'dan Sudan "Ina matukar farin ciki - ba zan iya bayyana farin ciki na ba. Za a gina sabuwar Sudan. Hakika abu ne mai kyau. Rayuwarmu za ta canza."

An wuni ana bukukuwa duk da ya ke sanya hannu bai dauki lokaci ba.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai dubban mutane da suka yi tafiya kilomita 300 daga Atbara, wanda shi ne birni na farko da ya fara zanga-zangar neman hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al Bashir.