Tabbatar Da Yin Adalci Shine Mafita Ga Najeriya – inji Bishop Stephen

Shugaban kungiyar Kristocin Najeriya CAN shiyyar Adamawa, Bishop Stephen Dami Mamza, ya bada tukwici ga yunkurin raya ‘kasa da kuma tabbatar da ci gaban ta.

Da yake magana da wakilin Muryar Amurka, Alphonsus Okoroigwe, Bishop Stephen ya godewa Allah da Ya sa aka shiga sabuwar shekara lafiya.

Ganin yadda aka fuskanci matsaloli da tashe-tashen hankali a shekarar da ta gabata, Bishop ya mika sakon fatan alkhairi ga daukacin ‘yan Najeriya, da kuma samun zaman lafiya a kasa baki ‘daya.

Sai dai kuma Bishop din yayi nuni da cewa, yin adalci tsakanin al’umma shine matakin da zai kawo hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya.

Domin karin bayani saurari hirar Alphonsus Okoroigwe da Bishop Stephen.

Your browser doesn’t support HTML5

Tabbatar Da Yin Adalci Shine Mafita Ga Najeriya – inji Bishop Stephen - 4'25"