Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Sun Kashe Mutane A Kauyen Kamale


Wani wajen da aka taba kai harin boko haram
Wani wajen da aka taba kai harin boko haram

Mutum hudu ne aka tabbatar an kashe a wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai garin Kamale da ke yankin Michika, daya daga cikin kananan hukumomin da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram a arewacin jihar Adamawa.

Yanzu mayakan Boko Haram sun dau sabon salon kai farmaki kauyukan da babu hanyar sadarwa, sannan kuma suke da sarkakiyar shiga a wuraren da aka koma na kananan hukumomin Michika da Madagali da ke kusa da dajin Sambisa dake zaman shelkwatar mayakan Boko Haram.

Harin baya bayan nan shine na dirar Mikiyar da suka yiwa kauyen Kamale da ke karamar hukumar Michika inda suka kashe mutum hudu da kuma sace dukiya. To amma kuma ba kowa ya sani ba, sabili da matsalar rashin hanyoyin sadarwa.

Cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya har da wani dan majalisar wakilan Najeriya, Mista Adamu Kamale da ke wakiltar mazabar Michika da Madagali, wanda sai da ya buya ta hanyar kwana akan duwatsu.

Rundunan 'yan sandan jihar Adamawan ta tabbatar da wannan sabon harin inda ta bukaci jama’a da su zama masu kulawa da ankara don kaucewa fadwa tarkon 'yan kungiyar ta Boko Haram. Kamar yadda Kakakin 'yan sandan jihar Othman Abubakar ya bayyana.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG