Taraba: An Kaddamar Da Taron Bita Ga Ma’aikatan Kiwon Lafiya Na Karkara

Ma'aikatan Kiwon Lafiya

Hukumar kula da kiwon lafiya matakin farko ta jihar Taraba tare da hadin gwiwar hukumar kula da kiwon lafiya ta ‘kasa matakin farko ta kaddamar da taron bita ga ma’aikatan kiwon lafiya dake aiki a karkara.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin jihar ke kaddamar da shirin rigakafin tafi-da-gidanka da ake gudanarwa a shingayen jami’an tsaro domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

karon farko kenan da ake gudanar da irin wannan taron bita na hadin gwiwar da zimmar koyawa ma’aikatan jinya sabbin dabarun sanin makamar aiki domin magance cututtukan dake addabar al’umma musamman a yankunan karkara.

Da yake gabatar da jawabinsa kwamishinan kiwon lafiya na jihar Taraba Dakta Innocent Vakkai, ya ce an shirya taron bitar ne domin inganta ilimin kiwon lafiya a bangarori daban-daban ga ma’aikatan jinya a jihar. Wanda ya ce hakan zai zo daidai da sabon tsarin kiwon lafiya da gwamnatin kasar ta kirkiro.

Kwamishinan Kiwon Lafiya Dr Innocent Vakkai, Jihar Taraba

Shima da yake nasa tsokacin shugaban hukumar kiwon lafiya a matakin farko a jihar Taraba, Aminu Jauro Hassan, ya ce hukumar za ta ci gaba da wayar da kan al’umma musamman kan muhimmancin tsaftace muhalli domin gujewa kamuwa da cututtuka tare da cin abinci mai kyau da zai inganta lafiyar jiki.

Haka nan Jauro Hassan, ya shawarci ma’aikatan kiwon lafiyan da aka horas da su yi amfani da abin da suka koya, domin cika gurbin da aka samu na kiwon lafiya a jihar.

Manazarta dai na alakanta matsalar rashin sanin makamar aiki da kuma rashin bada kai na iyaye da cewa suna taimakawa wajen rashin samun nasarar ayyukan rigakafi da kuma shirye-shiryen kiwon lafiya musamman a yankunan karkara, batun da masana ke cewa dole a tashi tsaye.

Domin ‘karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Taraba: An Kaddamar Da Taron Bita Ga Ma’aikatan Kiwon Lafiya Na Karkara - 3'22"