Taron Fahimtar Juna Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Nijar

  • Ladan Ayawa

NIGER: Taron Fulani Makiyaya

Bunkasar birane a 'yan shekarunnan na daga cikin matsalolin da ke raba manoma da makiyaya da filayensu a fadin Nijar. Game da wannan batun ne kungiyoyi tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar ne suka shirya taron domin neman mafita.

Kungiyoyin mazauna karkara da hadin gwiwar gwamnatin jamhuriyar Nijar, sun shirya wani taro da zummar lalubo hanyar warware matsalar da ake samu tsakanin manoma da makiyaya a jamhuriyar Nijar.

Masu shirya taron sun samar da taron ne da zummar ganin an samar da wasu yarjeniyoyi da za a bi sau-da-kafa domin kaucewa aukuwar rikici.

Shugaban kungiyar kare hakkin mutanen karkara, Jibo Banya ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Sule Mummuni Barma cewa fatarsu, taron ya cimma manufar sa.

Firayim Ministan Nijar, Biji Rafini ne ya jagoranci wannan tattaunawar da ya samun halarcin shugabannin al’umma dama wasu ‘yan majalisar dokokin kasar.

Ganin cewa Firayim Ministan na cikin wadanda suka halarci taron ne yasa wasu mahalarta taron bayyana masa wasu matsalolin da suke fuskanta musamman manoma.

Ga Sule Mummuni Barmada Karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Fahintar Juna Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Nijar 2'57