Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Neman Jami'an Gwamnatin Kamaru Da Aka Sace


Sojojin Kamaru a yankin da ake amfani da ingilishi
Sojojin Kamaru a yankin da ake amfani da ingilishi

An sace wasu jami'an gwamnatin Kamaru yayin da aka kashe wasu sojoji a ranar bikin matasa a yankin da ake magana da harshen ingilishi a arewa maso kudancin kasar.

Mahukunta a kasar Kamaru suna ci gaba da neman wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da aka sace ranar lahadi a yankin ‘yan awaren kuma ana zargin cewa ‘yan awaren ne suka sace su.

Sace wadannan jami'an ya biyo bayan kashe wasu jami'an soji ne da aka yi a ranar da ‘yan yankin masu magana da harshen ingilishi suka tada rikici bayan da jami'an kasar suka yi kokarin gudanar da bikin ranar matasa a yankin.

Wakilin Muryar Amurka, Moki Edwin Kinzeka ya ce, matar daya daga cikin jami'an gwamnatin kasar, Julienne Namata wadda mijin ta ne ke kula da yankin Batibo da ke yankin na ‘yan awaren, ta yi fatar cewa za ta ga mijinta ya dawo wanda aka dauka a cikin gidansu ranar lahadi a lokacin da yake shirin shiga cikin gari domin ya jagoranci bikin ranar matasa na karo 52.

Julienne ta ce da misalin karfe 8 na safe ne suka fara jin karar harbin bindiga, inda nan take ta tafi dakinsa domin ta sanar da shi abinda take ji amma sai ta tarar da baya ciki. Da kuma ta tambayi dan sandan da ke gadin gidan sai yace da ita sun fita shi da direbansa.

Mahukunta dai suna zargin cewa wasu ‘yan bindiga ne suka kai gashi Namata a cikin motarsa ba tare da sanin mai tsaron lafiyar sa ba.

Domin an ga motarsa ta kone kurmus amma shi ba a ganshi ba tun wannan lokacin kawo yanzu.

Absalon Manono Shugaban jami'an tsaron yankin Momo da ke gundumar Batibo inda wannan lamari ya faru, yace yanzu haka sun samar da tawagar bincike a wannan da dukkan jami'an tsaron da ke aiki a wannan gundumar tare da gudunmuwar gwamnan yankin da ma shugaban jami'an tsaro na daukacin yankin.

Yace kuma jami'an tsaron na iya bakin kokarin su domin bada dukkan gudunmuwar da ake bukata.

Wannan lamarin yasa da yawan matasan da ake bikin dominsu barin wannan yankin duk ko da kiransu da aka yi da su dawo.

Jami'an gwamnati da ‘yan majilisar dokokin dake wannan tyankin na ‘yan awaren sun jima suna fuskantar barazana sai dai wannan shine karo na farko da aka sace wani jamiin gwamnati.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG