Taron Kakakin Majalisun Dokoki A Afrika Ya Kuduri Aniyar Warware Matsalar Tattalin Arziki Da Nahiyar Ke Fuskanta

Speakers of parliament from African countries met in Abuja

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya shirya wani taro na shugabanin majalisun dokokin kasashen Afrika da zummar neman hanyar samar wa nahiyar sauki musamman a bangaren tattalin arziki ta hanyar yin magana da murya daya.

Wannan dai shi ne karo na farko da za a yi wannan taro a babban birnin tarayyar Najeriya. A lokacin da ya yi wa manyan bakin jawabin marhaba, kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya ce, idan masu yin dokoki suka hada kai wuri guda domin ci gaba, to irin wannan hadin kan ne Nahiyar Afirka ta ke bukata a fannin tattalin arziki, tsaro , kiwon lafiyar al'ummanta da walwalarsu, saboda haka ya yaba da wannan yunkurin.

Baya ga hadin kan, mataimakin kakakin majalisar wakilan Najeriya Ahmed Idris Wase, ya ce barkewar cutar korona ta kara dagula al'amura a Nahiyar idan aka yi la'akari da illar da ta yi wa tattalin arzikin kasashen Afirka da zamantakewa da siyasa, saboda haka akwai wata muhinmiyar bukata da wannan taron ke neman cimmawa.

Ku Duba Wannan Ma Zaben 2023: Masu Ruwa Da Tsaki Na Nuna Shakku A Zabukan Tsaida Yan Takara

Kakakin majalisar dokokin kasar Zimbabwe Jacob Frances Mudenda daya daga cikin mahalarta taron, ya nuna gamsuwar sa da irin wannan zumunci da suka kulla domin al'umman da kuma nemarwa kasashen su mafita da zata kai su ga bunkasan tattalin arziki.

Mudenda ya kara da cewa, fatar sa ita ce a matsayinsu na kakakin majalisun dokoki ya kamata su hada karfi da karfe wuri daya kana su tabbatar da ganin an ci gaba da wannan hadin kan domin amfanin al’ummar su a kasashen su.

Mataimakin shugaban kasa Forfesa Yemi Osinbajo ne ya bude taron kuma kakakin majalisu daga kasashen 14 ne suka halarci taron a ciki har da Ghana, Kamaru, Djibuti , Nijer da Zimbabwe..

Ga rahoton Medina Dauda daga birnin Abuja Najeriya:

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Kakakin Majalisun Dokoki A Afrika A Abuja