Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: Masu Ruwa Da Tsaki Na Nuna Shakku A Zabukan Tsaida Yan Takara


Farfesa Mshmoud Yakubu Shugaban hukumar zaben Najeriya.
Farfesa Mshmoud Yakubu Shugaban hukumar zaben Najeriya.

Ayayin da Hada hadar Siyasa ke ci gaba da kan kama a Nigeria masu ruwa da tsaki akan harkokin siyasar na ci gaba da nuna bukatar ganin jam'iyyun siyasar sun yi adalci a lokacin zaɓuɓbukan tsaida yantakara na jam'iyyun siyasa,

Masana harkokin siyasar dai sun ce daga wurin zaɓen fidda ƴan takara na jam,iyyu ne ake samun shugaba na gari da zai shugabanci al'umma ko kuma akasin haka,

Kwamred Ibrahim Tungan Wawa Mai Sharhi ne akan harkokin Siyasar Duniya yace kasahen da suka ci gaba jam'iyyu na zaɓen ƴan takarane akan cancanta ba wai ra'ayin wani ba.

Taron da shugabannin Najeriya suka yi domin tabbatar da zaman lafiya a zaben 2019
Taron da shugabannin Najeriya suka yi domin tabbatar da zaman lafiya a zaben 2019

A nashi bayanin, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi Ɗan Majalisar Dattawan Nigeria Mai Wakiltar Arewacin Jihar Neja da a yanzu yake buƙatar ganin jam'iyya ta APC ta sake bashi damar tsayawa takara dan komawa Majalisar yace indai za' a yi adalci baya da shakku sake komawa majalisa bisa la'akari da aikin da ya yi wa al'ummarsa.

Rumfar kada kuri'a a Najeriya a Yola a zaben 2019
Rumfar kada kuri'a a Najeriya a Yola a zaben 2019

Shima dai gwamna Abubakar Sani Bello dake neman Jam' iyyar APC ta bashi damar tsayawa takarar neman kujerar majalisar dattawan daga Arewacin Nejan yace duk da APC ta samu karbuwa sosai ga Jama'a, a lokacin zaben fidda gwani lamarin na bata ruwa.

A yanzu dai manyan jam'iyyun siyasar dake gogayya da juna a Nigeria wato APC da PDP sun bada tabbacin yin adalci a lokacin zaɓuɓɓukan fidda ƴan takarar. Yayinda hankalin 'yan Nigeria ya karkata ga masu zaben fidda ƴantakara na ja,miyyun siyasar Nigeriar.

Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG