Taron Kasa Na Iya Kara Rarraba Kawuna: Sen Maccido

Bukukuwan Ranar Samun 'Yancin Najeriya.

Shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar dattijan Najeriya Ahmed Muhammad Maccido ya bayyana cewa, bai ga amfanin taron tuntuba na kasa da ake shirin yi a Najeriya ba.
Shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar dattijan Najeriya Ahmed Muhammad Maccido ya bayyana cewa, bai ga amfanin taron tuntuba na kasa da ake shirin yi a Najeriya ba.

Saneta Maccido yace idan ba a yi hankali ba taron yana iya kara rarrabuwar kawuna a maimakon cimma manufar da ake tsammani. Bisa ga cewarshi, wadansu suna iya zuwa su kasa kai zuciya nisa a maimakon gyara su rika zagin juna.

A cikin hirarsu da Sashen Hausa yayin wata ziyara da ya kawo tashar, Saneta Maccido yace kowanne bangare zai dandana kudarshi idan Najeriya ta rarrabu kamar yadda wadansu suke neman ganin an yi.

Da yake magana dangane da dambarwar siyasar jam’iyarsu ta PDP, dan majalisar ya bayyana cewa, abinda ya kawo sabani tsakanin ‘yan jam’iyar shine rashin tattaunaw da kimanta gaskiya da adalci. Ya kuma ce batun cire shugaban jam’iyar Bamanga Tukur da kuma batun tsayawa takarar shugaba Goodluck Jonathan batutuwa ne da suke takarda kawai amma akwai batututwa da dama da ‘ya’yan jam’iyar da suka balle suke neman ganin an yi kafin a koma inuwa daya.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira Da Saneta Ahmed Muhammad Maccido - 3:50