Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Kawai Ba Za Su Iya Kawo Zaman Lafiya A Nijeriya Ba.


Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan

Wasu manya a Nijeriya sun lura cewa muddun hukumomi da jama'a ba su sauke nauyin da ya rataya a wuyan su ba, sojoji ba za su iya tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya ba.

Wasu yanyan ‘yan Nijeriya sun ce fahimtar juna da kuma hakuri da juna ne kadai za su kai Nijeriya ga gaci amma ba ikon hukuma ba. Manyan ‘yan Nijeriyar, wadanda aka karrama wasun su cikin wani littafi mai suna “Mazan Kwarai Da Su Ka Yi Aiki Da Gaskiya Cikin Al’umma” da Furfesa Cefas Tushima na Cibiyar Koyar da Tauhidin Addinin Kirista da ke Jos ya rubuta, sun ce wajibi ne kowani dan Nijeriya ya ba da ta sa gudunmowa wajen gina kasa idan ba haka ba babu abin da zai gyaru.

Wakiliyarmu ta Jos Zainab Babaji, wadda ta aiko da labarin, ta ruwaito daya daga cikin wadanda aka karrama a littafin wato tsohon babban kwamandan dakarun tabbatar da zaman lafiya na ECOMOG da aka tura kasar Saliyo, Janar Martin Luther Agwai, ya na cewa babu wani irin ikon hukuma ko soji da zai tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya in ba a daidaita wasu al’amura ba da su ka hada da kiwon lafiya da ilimi da tattalin arziki da kuma siyasar ita kan ta.

Shi ma Gwamnan jihar Kaduna, ta bakin mai ba shi shawara ta bakin abubuwan da su ka shafi addinin Kirista, Rabaran John Joseph Hayab, ya ce kowani dan Nijeriya ma shugaba ne a irin matsayin da ya ke. Don haka, ya ce muddun ana so a gyara kasar sai kowa ya taka tasa rawar. Haka zalika, Sakataren darikar ECWA na kasa baki daya furfesa Samuel Kunyob y ace hakkin aiktata gaskiya ya rataya a wuyan kowa har da masinjan ofis.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG