Taron Kyautata Dangantaka Tsakanin Kasar Najeriya Da Nijer

Shugaban kasar Najeriya Buhari da shugaban kasar Nijer Issoufou a Niamey.

An kaddamar da wani taro don kara fahimta da kyautata dangantaka tsakanin kasar Najeriya da kasar Nijar.

Sanin kowane cewar dangantaka tsakanin kasashen Najeriya da Nijar, tsohuwar dangantakace tun shekaru aru-aru. Hakan ne yasa kasashen suke gudanar da wani taro a karshen kowace shekara, don gano hanyoyi da za’a kyautata danganta a tsakanin kasashen biyu. A taron wannan shekara karo na 39, ya maida hankali ne wajen gano yadda za’a karfafa harkokin tsaro, shige da fice na ‘yan kasashen biyu a kowane lokaci.

Shige da fice na miyagun kwayoyi, harkar safarar mutane, kana da yadda wasu ‘yan kasar Najeriya ke shiga kasar ta Nijar don neman hanyar shiga kasar libiya da zumar tafiya kasashen turai. Alh. Girema Kura, wanda yake wakiltar kasar Nijar a wajen taron ya bayyanar da muhimancin wannan taron a dai-dai wannan lokaci da harkar tsaro take neman lalacewa a tsakanin al’umar kasashen biyu.

Ya bayyanar da cewar suna wannan taron ne don ganin yadda za’a inganta tarayya batare da anbar miyagu sun shiga harkar ba. Haka suna kokarin isar da sako ga al’umar kasashen biyu, da su kokarta wajen ganin sun kyautata dangantar ‘yan kasashen biyu musamman a harkar cinikayya, noma, kiwo da sauran harkokin yau da kullun. Burin da ake kokarin cimma a wannan taron na ministocin kasashen biyu shine al’umar kasashen su shiga kowace kasa batare da wani tsangwama ba.

Ambasada Abubakar Abduljalil Sulaiman, sakataren hukumar hadin gwiwan kasashen biyu, ya bayyanar da matsalar tsaro a matsayin abun da taron wannan shekarar zai maida hankali a kai matuka. Haka kuma sau da dama mutane daga Najeriya kan saci kudin azrikin kasa su kuma yi amfani da kasar Nijer wajen fataucin arzikin, duk dai suna sa ran wannan abubuwan da basu daceba sun kawo karshe.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Da Nijar - 2'36"