Tasirin Taron Tattalin Arziki na Duniya

Firayim ministan China Li Keqiang, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da Klaus Schwab.

A yau ne ake kammala taron tattalin arziki na duniya da ake yi a Abuja,wanda yayi sanadiyar tsayiwar hada-hadar kasuwanci
A yau ne ake kammala taron tattalin arziki na duniya da ake yi a Abuja,wanda yayi sanadiyar tsayiwar hada-hadar kasuwanci, don dama gwamnati ta bada hutun kwana uku don rage cunkoson a birnin da zai tabbatar da tsaro.

Wani ma’aikaci da ya nisanci birnin a lokaci taro yace” gwamnati tasa doka na kwana uku kowa ba zai bude wurin sana'arsa ba,har bankuna da ma’aikatun gwamnati an kule,to ni,ina so inje Abuja, amma na hakura ba don komai ba saboda in nemawa kaina sauki don gwamnati tace a zauna a gida saboda bana so inje garin shiga in samu matsala da jami’an tsaro ko kuma in samu matsala a hanya wanda yana iya jawo mi bacin rai,ko kuma wani abu makamancin wannan."

Ya kara da cewa "dalili kennan da yasa na zauna a gida sai bayan Allah yasa an gama taron nan lafiya sanan inje in ci gaba da harkokin na a cikin garin Abuja."

Farfadowar Abuja dai zai kai litinin mai zuwa,don da dama ma’aikata sun yi amfani da damar wajen yin tafiye-tafiye ko kuwa ziyartan kauyukansu.

Dakta Kole Shattima, na asusun Mccartha foundation,na karfafa riban taron inda yace ma’aikatan gwamnati watakila ba zasu ji zafin sa ba,saboda ko sun je aiki ko basu je ba za’a biyasu.

Gani a kasa wajen saukowar farashi kayayyaki,wutar lantarki da man fetur ne zasu iya dawo da akasarin alumar kasar dake rayuwa kasa da dala daya a yini wato kimanin Naira dari da sittin.

Your browser doesn’t support HTML5

Tasirin Taron Tattalin Arziki na Duniya - 3'00"