Tattalin Arzikin Duniya Ya Shiga Mawuyacin Hali Sanadiyyar COVID-19

Bincike ya nuna cewa kusan daukacin tattalin arzikin duniya ya shiga wani mawuyacin hali sanadiyyar annobar cutar coronavirus.
Sai dai bincike ya kuma gano cewa, wasu kasashe sun fi wasu kimtsawa wajen daukan matakan da za su kare harkokin kasuwanci da ma’aikatansu daga radadin da ke biyo bayan barkewar cutar ta COVID-19.
Korea ta Kudu, Singapore da Vietnam na daga cikin kasashen da a ake misali da su wajen daukan matakan gaggawa a lokacin da cutar ta barke, inda suka yi maza-maza suka rufe wuraren kasuwancinsu, suka kuma dukufa wajen gudanar da gwaje-gwaje tare da bibiyar wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu da cutar
Masana tattalin arziki sun ce a dalilin hakan, ya sa kasashen suka samu saukin bude wuraren kasuwanci ba tare da wata wahala ba.
Su ana su bangaren kasashen da suka ci gaba a nahiyoyin Asiya, Turai da kuma arewacin Amurka, gwamnatoci sun fi mayar da hankali ne wajen ba da tallafin agazawa tattalin arziki ga wuraren kasuwanci da kuma ma’aikatan da suka rasa ayyukansu sanadiyyar rufe wuraren kasuwancinsu
Kasashe irin Jamus, sun yi nasarar rage yawan wadanda suka rasa ayyukansu ta hanyar ba kamafanonin tallafin da za su ci gaba da biyan ma’aikatansu.
Anan Amurka, wacce take fuskantar babbar matsalar tururuwar wadanda suka rasa ayyukansu, ana ba ma’aikatan tallafi ne karkashin wani shiri na wadanda suka rasa ayyukanszu, duk da cewa akwai matsaloli da aka fuskanta na wadansu da ba sa cin gajiyar shirin.
Sai kasasashe masu tasowa, wadanda suke fama da matsalolin talauci tun gabanin barkewar cutar ta COVID-19, ana fuskantar mummunan yanayi tun da aka samu nakasu a fannin fitar da kayyaki zuwa kasashen waje da kuma durkushewar fannin yawon bude ido, lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta saka kokon barar neman tallafin dala biliyan bakwai domin a kai wa kasashen da suka fi tagayyara agaji