Tawagar Turai Ta Ce Ba Za Ta Fifita Wani Bangare A Zaben Najeriya Ba

Yayin da ake kidaya kuri'a a wata rumfar kada kuri'a a garin Yola na jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya

Jami'an tawagar Tarayyar Turai da za su sa ido a babban zaben Najeriya, sun ce basa goyon bayan wani dan takara ko wata jam'iyya a zaben da za a yi a watan gobe.

Yanzu haka tawagar masu sa ido daga Tarayyar Turai a karkashin jagorancin Uwargida Maria Arina tace, basu zo Najeriya domin goyon bayan wani dan takara ba.

Maria tace, aikin su shine tattara bayanai kan yadda za’a gudanar da zabe, ta kuma kara da cewa tawagar bata da wata sha’awa ta yadda zaben zai kasance.

Sanann tace, tawagar tana cin gashin kanta, kuma bata da wata alaka ko ra’ayi na wani dan takara a wannan zabe, domin mu babu ruwanmu kuma mun fitar da matsayar mu akan wannan, a matsayin mu na jamia’an Tarayyar Turai.

Ministan Labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya ce, gwanmati ta samu wasu bayanan sirri da ke nuna cewa, akwai wasu da ke kitsa mummunan tashin hankali a kasar yayin wannan zabe.

Lai ya ce, sun gano masu son tada husumar ta hanyar amfani da mayakan Boko Haram da ‘yan bindiga.

Wannan gargadi na gwanmatin Najeriya ya zo ne a daidai lokacin da jami’an kasashen duniya suke kokarin saka ido akan zaben da za’a gudanar a watan gobe.

Saurari cikakken taroton Hassan Maina Kaina:

Your browser doesn’t support HTML5

Tawagar Turai Tace Baza Ta Fifita Wani Bangare A Zaben Najeriya