TEXAS: Gwamnatin Na Binciken Mutanen da 'Yansanda Suka Harbe

Jami'in FBI mai bincike yana yiwa 'yansanda tambayoyi

Gwamnatin Amurka tana binciken mutanen nan biyu da 'yansandan jihar Texas suka harbe har lahira

Mahukuntar gwamnatin tarayyar Amurka yanzu haka suna binciken wasu muttane biyu da yan sanda suka kashe a Texas bayan da mutanen suka harbi wani mai gadi dake wajen wurin wani bikin gabatar da jawabai.

Yan sanda suka ce wadannan mutanen biyu dai suna zaune wuri guda, watoElton Simpson da Nadir Soofi dukkansu yan jihar Arizona ne dake kudancin Amurka.

Wasu bayanan kotu sun nuna cewa dama shi Simpson yana karkashin wani binciken sirri da ake yi masa tun a cikin shekarar 2006, wanda a shekarar 2010 aka yanke masa hukuncin shirga karya ga hukumar binciken manyan laifuka ta nan Amurka game da ra’ayin sa na shiga kungiyar yan ta’adda dake Somalia.

Hukumar ta FBI dai da hadin gwiwar yan sanda sun binciki gidan wadannan mutanen biyu a Phonix, inda suka hana gilmayya a kusa da gidan kana suka fitar da sauran mutanen dake cikin wannan gida har na tsawon awoyi.

Joe Harm , mai magana da yawun rundunar yan sandan Texas yace duk da yake ba’a gano dalilin da yasa su kai wannan harin ba, amma dai abinda aka tabbatar shine sunzo wannan waje ne domin kawai su harbi mutane.