Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TEXAS: 'Yansanda Sun Kashe Wasu 'Yan Bindiga


'Yansanda na gadin harabar makarantar da aka yi gasar zanen Annabi Muhammad (SAW)

'Yansanda sun kashe wasu da suka budewa masu gadin wata makaranta wuta

‘Yan sandan a jihar Texas dake kudancin Amurika sun kashe wasu ‘yan bindiga biyu, da suka bude wuta akan masu gadin wata makaranta a daren jiya Lahadi, a wajen gasar zanen borkwanci kan annabi Muhammad (SAW).

A cikin birnin Garland, dake wajen Dallas ance wani jami’in tsaro ya sami rauni kuma ana cigaba da dubawa kasancewar za’a iya samun bom a motar da ‘yan bindigar suka yi amfani da ita. Jami’ai dai basu tabbatar da ko suwaye ‘yan bindigar ba. An yi jinyar ‘dan sandan a sibiti kuma har an sallame shi.

Kungiyar dake hankoron fadin albarkacin baki da ake kira American Freedom Defense tace ta shirya wannan gasa, kuma ta yi alkawarin baiwa duk wanda ya lashe gasar kudi dala dubu goma.

Mutane dai sun zuba hotan bidiyon borkancin sama da 350 saboda gasar.

XS
SM
MD
LG