Theresa May Ta Karawa 'Yan kasashen Turai Kwarin Gwiwa

Firai minsitar Birtaniya, Theresa May

Firai ministar Birtaniya Theresa May, ta yi kokarin ba miliyoyin ‘yan kasashen Turai dake zama a kasar tabbacin cewa, rayuwarsu da ta iyalansu ba za ta sauya ba, bayan da kasar ta fara shirin ficewa daga kungiyar tarayyar Turai a 2019.

Firai ministar Birtaniya Theresa May ta ce rayuwar 'yan kasashen turai da iyalansu ba za ta sauya ba duk da cewa kasar na shirin tattara inata-inata ta fice daga kungiyar tarayya ta EU, bayan da aka kada kuri'ar raba gardama a bara.

May ta yi tayin ba ‘yan asalin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai ‘yancin zama a Birtaniyar kamar kowanne bature da aka haifa a Ingila, da wadanda aka haifa Scotland da kuma Wells, da kuma damar kula da lafiyarsu da ilimi, da tallafin marasa galihu, da kuma kudin fensho.

Za a yi amfani da dokokin kasar Birtaniya a kan al’ummomin kasashen Kungiyar ta EU, ba tare da an yi la’akkari da dokokin kotunan kasashen Turai ba.

A wani sako da ta gabatar, May ta fadawa kimanin ‘yan kasashen turai miliyan 3.1 dake zaune a Birtaniya cewa, "Muna so ku zauna."

Ta kara da cewa burinta shine ta ba dukan wadanda suke zaune a Birtaniya a halin yanzu tabbacin cewa, ba za a ce su fice daga kasar ba lokacin da Birtaniya za ta fice daga kungiyar.