Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban CBN

Godwin Emefiele (Hoto: Facebook/CBN)

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da sanarwar dakatar da Mista Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) daga aiki nan take. 

Wannan mataki ya zo ne a sakamakon binciken da ake yi a ofishinsa da kuma yin gyare-gyare a fannin hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar.

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya Mista Willie Bassey ya fitar ta bayyana hakan.

Shugaban CBN, Godwin Emefiele

A cewar sanarwar, shugaba Tinubu ya umurci Mista Emefiele da ya gaggauta mika ragamar mukaminsa ga mataimakin gwamna (Operations Directorate). Mataimakin gwamnan zai yi aiki a matsayin mukaddashin gwamnan babban bankin kasa CBN har sai an kammala bincike da aiwatar da gyare-gyaren da aka tsara.