Trump, Biden Na Jimamin Rasuwar Ginsburg

Marigayiya, Mai Shari'a Justice Ruth Bader Ginsburg ta Kotun Kolin Amurka (AP…

Ana ci gaba da nuna alhini dangane da rasuwar Mai Shari’a a kotun kolin Amurka Justice Ruth Bader Ginsburg, wacce ta rasu a ranar Juma’a tana mai shekara 87.

Rasuwar Ginsburg, wata dama ce da Shugaba Donald Trump ya sake samu a karo na uku, ta fadada rinjayen masu ra’ayin mazan jiya a kotun kolin Amurka, yayin da wasu ke ganin kasar na fama da rarrabuwar kawuna, a kuma daidai lokacin da ake tunkarar zabe kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito.

Ginsburg ta yi “rayuwa mai ban mamaki, babu abin da za a iya cewa, illa a ce, mata ce mai ban mamaki,” shugaba Trump na jam’iyyar Republican ya fadawa manema labarai bayan da ya samu labarin rasuwar bayan kammala wani gangamin yakin neman zabe a jihar Minnesota, inda ya kara da cewa yana mai cike da bakin cikin wannan rashi.

A kuma wata sanarwa da ya fitar, shugaban ya kara da cewa, Amurka, “na alhinin rashin wata jaruma a fannin shari’a.”

Ana shi bangaren, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Democrat Joe Biden, ya kwatanta marigariyar a matsayin wacce “ta tsaya tsayin daka ba tare da nuna tsoro ba a fafutukar kare hakkin kowa da kowa, yana mai cewa irin akidar da ta tsaya akai, za ta ci gaba da yin tasiri a fannin shari’a na wani tsawon lokaci.

Tun dai a shekarar 1993 aka zabi Ginsburg a matsayin daya daga cikin Alkalan kotun kolin Amurkan.