Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Rukunin Matasan Amurka, Cutar COVID-19 Ta Fi Kama Tsirarun Jinsi


Wasu matasan Amurka sanye da kyallen kariya
Wasu matasan Amurka sanye da kyallen kariya

Kamar yadda tsirarun jinsi su ka fi Turawa kamuwa da cutar a Amurka a bangaren manya, a bangaren matasa ma haka abin ya ke, tsirarun jinsi sun fi kamuwa.

Wasu alkaluma da Cibiyar Kare Yaduwar Cututtuka ta CDC ta fitar anan Amurka a wannan makon, sun nuna cewa cutar COVID-19 ta fi kama mutane ‘yan kasa da shekara 21 wadanda suka fito daga cikin al’umomi marasa rinjaye idan aka kwatanta da takwarorinsu fararen fata masu makamantan wadannan shekaru.

Daga ranar 21 ga watan Fabrairu zuwa 31 ga watan Yuli, mutum 121 ‘yan kasa da shekara 21 ne suka mutu sanadiyyar cutar kamar yadda alkaluman da aka tattaro daga jihohi 27 suka nuna.

Sama da kashi 75 cikin 100 na wadannan matasan Hispaniyawa, bakaken fata, Indiyawan Amurka da kuma asalin mazauna yankin Alaska, duk da cewa adadin wadannan al’umomi su ne kashi 41 na yawan al’umar Amurka.

Da aka kara kasafta alkaluman, an gano cewa yaran Hispaniyawa suke da kashi 44 cikin adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar ta coronavirus, sai yaran bakaken fata da ke da kashi 29, idan aka kwatanta da kashi 14 na yaran fararen fata da cutar ta kashe.

A gefe guda kuma Indiyawan Amurka da asalin mazauna yankin Alaska suke da kashi hudu, yayin da su ma Asiyawa da mazauna tsibiran yankin Pacific ke da kwatankwacin wannan adadi.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG