Trump Ya Zargi Shugaban Bankin Ajiyar Amurka Da Rashin Kula

A wannan makon kasuwar hada-hadar hannaye jari a Amurka, sun yi mummunar faduwa da ba'a taba ganin irinta ba cikin shekaru goma.

Kasuwar hada-hadar hannayen jari a Amurka ta fadi a jiya Litinin, inda ma’aunin saye da sayarwar yayi kasa da maki dari biyar wato kashi biyu cikin dari.

A nasa bangaran, Shugaba Donald Trump ya dora laifin faduwar kasuwar a kan rashin gudanar da ayyuka daidai da bankin ajiya da wasu kalubalen tattalin arziki.

A wani sako Twitter da ya aika, yana cewa tattalin arzikin Amurka kadai ne yake samun matsala saboda samun karuwar kudin ruwa.

Shugaba Trump, ya zargi shugaban bankin ajiyar Jerome Powell da rashin sanin yadda kasuwar take da kuma rashin kula da tattalin arziki da tsadar kudin ruwa da ake dorawa rance.

Bankin ya rage kudin ruwan da ake dorawa rance kusan kasa da kashi daya, domin bunkasa ci gaba tattalin arziki a lokacin da kasar ta fuskanci matsalolin tattalin arziki a shekarar 2007.

Bankin ya ci gaba da rike kudin ruwa mafi kankanta tsawon shekaru bakwai.