Trump: Za Mu Bada Fifiko Ga Baki Masu Ilimi Akan Masu Dangi

Sabon tsarin shugaba Trump, zai bar adadin masu katin iznin zaman kasar na dindindin–Green Card.

Ana sa ran a yau Alhamis, shugaban Amurka Donald Trump, zai sanar da wani tsari, wanda aka dade ana jira, game da batun shige da fice a Amurka.

Wannan tsarin, zai sa hukumomi su daina mayar da hankali, kan masu neman shiga kasar saboda suna da dangi ko kuma wani dalili da ya shafi neman agaji.

Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, gabanin sanarwar da shugaba Trump, zai yi da tsakar rana a yau, wani babban jami'in gwamnatin Trump ya ce, shirin zai taimaka wajen karfafa tsaro a kan iyakoki da kuma samar da sahihin tsari, yana mai cewa lamarin zai zama na “gogayya ne."

Wannan tsari na Trump, zai bar adadin masu katin iznin zaman kasar na dindindin – wato masu Green Card, a kan miliyan-daya-da-dugo-daya.

Amma kuma zai fi mayar da hankali kan yadda ake ba da katin iznin zaman kasar, inda za a fi ba da fifiko ga mutanen da ke da wata kwarewa, masu ilimi da ke da yiwuwar samun aiki ko kuma zuba hannayen jari a Amurka, a maimakon a ce ana duba dalili na dangantakar da ke tsakanin dan Amurka ko kuma wata bukata ta neman agaji.