Wannan na zuwa ne lokacin da ‘yan bindiga ke ci gaba da kisa da garkuwa da manoma, yayin da wasu jama'a suka shafe shekaru zaune ba abin yi saboda matsalar ta rashin tsaro.
Matsalar rashin tsaro dai ta jima tana kawo koma baya a Najeriya musamman a jihohin arewa.
Yankin arewa, yanki ne wanda ya yi fice wajen noman abinci, wanda gwamnatoci da yawa ke cewa suna baiwa muhimmanci da karfafa guiwar manoma, sai gashi wasu manoma sun shafe shekaru zaune a banza saboda barayi sun hana a shiga gonaki a yi noman kamar yadda wani manomin Isa ta jihar Sakkwato wanda ya tsallake rijiya da baya ya bayyanawa Muryar Amurka. Yace shekarar sa 4 zaune ba abin yi saboda barayi sun hana noma ko fita a yi kasuwanci yanzu da ya sa abinda aka ci ya zama da wahalar samu.
A hirar shi da Muryar Amurka, dan Majalisa mai wakiltar yankin Isa a Majalisar dokoki ta jiha Habibu Halilu Modaci ya ce ba wai hana noma ne kawai barayi suka yi ba har da kisan manoman idan suka shiga gonakki wurin aiki.
Yace ko a wannan mako barayi sun kashe wasu mutane da kuma yunkurin yin garkuwa da wasu lokacin da suka je gona wurin aiki.
Wannan yanayin dai ya jima yana damun jama'a, sai dai gwamnati mai ci yanzu ta yi alwashin kawar da matsalolin rashin tsaro a Najeriya duk da yake gwamnatin da ta gabata ma ta yi irin wannan alwashin wanda ta kasa cikawa.
Masana lamurran tsaro kamar Dokta Yahuza Getso na ganin idan gwamnatin Najeriya da gaske ta ke yi dole sai ta nuna da gaske take yi don akwai kalubale a hanyar da ake sama yanzu idan zata samu mafita.
Yankuna da dama ne a arewacin Najeriya ke fuskantar wannan matsalar ta ‘yan bindiga su hana shiga gonaki, abinda kuma kan iya ci gaba da mayar da hannun agogo baya ga kokarin wadatar da kasa da abinci da gwamnati ke muradin cimma.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5