Turawa Masu Saka Ido A Zaben Najeriya Sun Isa Kasar

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Mr. Geoffrey Onyeama

Jami'ai daga Tarayyar Turai sun isa Najeriya, domin saka ido kan zabubukan da za a gudanar a kasar a watan gobe.

Wata tawagar Tarayyar Turai da za ta sa ido akan babban zaben Najeirya da za a yi a watan gobe, ta iso Abuja babban birnin kasar, tawagar ta na karkashin jagorancin Uwargida Maria Arina, kuma tuni har mambobin tawagar sun gana da Ministan Harkokin Wajen Najeriya Mr. Geoffrey Onyeama, a ma'aikatar da ke Abuja.

Maria Arina ta ce, Najeriya na da kima da daraja sosai a idon kasashen duniya, don haka zaben na watan gobe na da matukar muhimmanci, duba da ganin matsayin Najeriya a tsakanin idanan duniya.

Sannan tace akwai bukatar a gudanar da zabe na gaskiya da adalci, kuma a halin yanzu babban abinda ‘yan Najeriya su kafi bukata shi ne su aminta da wannan tsari.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, ya tabbatarwa da Tarayyar Turai cewa, za a gudanar da zabe na gaskiya da adalci, kuma wanda duniya zatai na'am dashi.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Turawa Masu Saka Ido A Zaben Najeriya Sun Isa Kasar