Wadanda Suka Kubuta Da Rayukansu A Yola Sun Bayyana Yadda Bam Ya Tashi

Harin bam na kwanakin baya a Yola.

A wani gefen kuma, hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce adadin wadanda aka kashe a wannan harin ya karu zuwa mutum 34.

Mutanen da harin bam na ta'addanci ya rutsa da su a Yola, Jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya a daren talata, wadanda kuma suke kwance su na jinya yanzu haka a asibitin kwararru na Yola, sun bayyana yadda aka yi wannan ukuba ta rutsa da su.

Wani wanda ya ji rauni a hannu, yace yana shigewa da motarsa ne ta wurin da bam din ya tashi, kawai sai ya ji karar tashin bam din, amma daga nan bai san abinda ya faru ba sai ya tsinci kansa a gadon asibiti. Shi wannan bawan Allah likitoci sun ce kashi ne ya karye ya shiga cikin naman hannunsa.

Wani matashi ma, yace ya je shi karbar baturin wayarsa ne, sai bam din ya tashi ya rutsa da shi, shi ma ya tsinci kansa a asibiti.

Wani dattijo mai suna Mohammed Ibrahim yace su na zaune su na hira da wasu jama'a sai ya ji karar tashin bam din. ya ce bai ma san abin ya taba shi ba sai da ya ji wani abu mai sanyi a jikinsa, sai ya gano cewa jini ne ke kwarara daga jikin nasa.

Wannan lamarin yana zuwa a daidai lokacin da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, take fadin cewa cikin dare, biyu daga cikin mutanen da suka ji rauni a wannan harin bam sun mutu a asibiti.

Wannan shi ya kawo adadin mutanen da 'yan ta'addar suka kashe zuwa 34 a yanzu.

ga cikakken rahoto daga bakin Ibrahim Abdul-Aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Adadin Wadanda Suka Mutu A Yola Ya Karu Zuwa 34 - 3'38"