Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Shekara 14 Ta Wallafa Littafi Kan Marayu


Wasu Marayu a wani wuri da ake kula da marayu.
Wasu Marayu a wani wuri da ake kula da marayu.

A Najeriya matsalar Boko Haram ta yi sanadiyar mutuwar dubban mutanel lamarin da ya sa ake samun dumbin yara marayu a arewa maso gabashin Najeriya.

Yayin da adadin marayu sai karuwa ya ke yi sakamakon iyayen yara da Boko Haram suka kashe a arewa maso gabashin Najeriya.

Wata yarinya ‘yar shekara 14 ta bi sawun kungiyoyin sa kai ta hanyar wallafa littafi wanda ta yi wa lakabi da jimamin marayu da niyyar kafa gidauniyar da za ta rinka tallafawa marayu.

Mawallafiyar littafin, A’isha Bukar Kiri daliba ce, ‘yar aji uku a makarantar sakandare na barikin sojoji da ke Yola, ta kuma ce jigon littafin shine irin halin zaman kewa da kadaici da marayu ke fuskanta.

Ta ce ta gina littafin ne akan irin halin da ta sami kan ta a ciki lokacin da iyayenta suka rasu tun tana karama.

Wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu na da karin bayani a wanan rahoto da za ku ji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

XS
SM
MD
LG