Wadanne Kalubale Ke Gaban Sabon Shugaban Kungiyar ECOWAS?

Shugaba Issouhou Mahamadou

Sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yamamcin Afirka ta ECOWAS Issouhou Mahamadou, wanda shi ne shugaban Nijar, ya lashi takobin magance wasu manyan matsalolin da yake gani suna hana tafiyar da sha’anin tattalin arzikin kasashen yankin Afirka ta yamma.

A ganin shi cikin matsalolin, akwai babbar matsalar ta’addanci, dora shirin samar da kudade na bai-daya da mambobin kungiyar za su rika amfani da su da dai sauransu.

A karshen makon da ya gabata aka zabi Shugaba Issouhou a taron kungiyar na 55 da ya gudana a Abuja, babban birnin Najeriya.

Ministan harkokin wajen Nijar Kalla Hankourao ya yi wa wakilin Muryar Amurka a birnin Yamai Souley Mumuni Barma karin haske kan batutuwan da shugaban zai tunkara.

Your browser doesn’t support HTML5

Wadanne Kalubale Ke Gaban Sabon Shugaban Kungiyar ECOWAS?