Bayan da suka kalli bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar wasu iyayen Chibok sun gane fuskokin 'ya'yansu a cikin bidiyon.
WASHINGTON, DC —
Wasu iyayen yaran Chibok da suka kalli bidiyon da Boko Haram ya fitar sun ce sun iya gano 'ya'yansu.
Bidiyon ya dauki hankulan jama'a da dama musamman iyayen yaran da aka sace. Tun lokacin da aka fitar da bidiyon gwamnatin jihar ta umurci iyaye da su je fadar gwamnati domin su karbi bidiyon.
Wani Mr. Samuel wanda 'yaruwarsa na cikin wadanda aka sace yace kawo yanzu sun gano fuskokin 'ya'yan nasu guda biyu a cikin bidiyon, wato Hamsu Abubakar da Aisha Abubakar. Yace suna addu'ar Allah Ya kubutar da su. Ban da shi Samuel akwai wasu iyayen ma da suka gano nasu.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5