Wasu Manyan Jahar Filato na Kuka da Jam'iyyar Su ta PDP

PDP

Masu kukan na zargin gwamna Jonah Jang da siyasar dauki dora.

Wasu 'yan jam'iyar PDP a jahar Filato sun bayyana takaicin su kan yadda shugabanni ke tafiyar da harakokin jam'iyar a matakin jahar musamman ma a tarurrukan zaben wakilan da za su yi zaben fidda gwani a zabubbuka masu zuwa.

Tsohon gwamnan jahar Filato Ambassador Fidelis Tapgun ya ce jama'ar jahar ce kadai ke da hurumin zaben wadanda ta ke so su shugabance ta.

Wakiliyar Sashen Hausa a jahar Filato Zainab Babaji ta tambayi Ambassador Fidelis Tapgun ko me ya sa jam'iyar PDP ke dari-dari da su?

Your browser doesn’t support HTML5

Ambassador Fidelis Tapgun ya koka da siyasar su ta PDP a jahar Filato. - 4':28"