Accessibility links

PDP Tace Batayi Mamaki Tambuwal Ya Koma Jam'iyyar APC Mai Hamayya Ba

  • Aliyu Imam

Kakaki Aminu Waziri Tambuwal ya zanta da Muryar Amurka.

Daya daga cikin jiga jigan jam'iyyar tsohon senata Jonathan Zwingina yace jam'iyyar tayi bakin cikin haka.

Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya tace bai zo da mamaki ba ganin kakakin majalisar wakilai ta tarayya Aminu Waziri Tambuwal ya bar jam'iyyar zuwa babbar jam'iyyar hamayya ta APC.

Jiya talata ce kakakin majalisar wakilai Tambuwal ya bayyana canza shekararsa a zaman majalisar, wanda daga nan ne ya dage zaman majalisar sai cikin watan Disemba.

Da yake maida martani kan wannan mataki, Zwingina yace PDP tayi bakin cikin rashinsa, duk da haka ba zata dauki matakin muzgunawa, ko kuntatawa Tambuwal ba, domin akwai yiyuwar ya sake dawowa PDP.

Senata Zwingina yace, kada kakain majalisar ya manta cewa fa PDP ce ta kawo shi majalisar wakilai, saboda haka dukkan abunda ya zama, sanadiyyar haka PDP ce.

Ga karin bayani

XS
SM
MD
LG