Wasu Yan Bindiga Sun Kaiwa 'Yan Shi'a Hari A Afghanistan

An bada rahoton cewa wasu yan bindiga da suka yi shigar burtu sanye da rigunan yan sandan kasar Afghanistan sun kutsa wani wurin ibadar yan Shi’a dake cike da mutane a jiya Talata, da dare suka kashe mutane goma sha hudu da raunana fiye da mutane talatin.

Jami’ai da shedun gani da ido sunce wani mai harin kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a lokacinda aka fara sumamen a yankin Karte-e Sakhi na Kabul baban birnin kasar, a yayinda jami’an tsaro suka harbe masu harin kunar bakin wake guda biyu. Jami’an kiwon lafiya sun tabbatar cewa akalla mata goma sha takwas suna daga cikin wadanda suka ji rauni da aka kai asibiti.

Jiya Talata tara ga wata muharram, kuma galibi yan Shiya a duk fadin duniya su kan yi gangami a ranakun tara da kuma goma ga watan muharram domin juyayin kashe jikan Annabi Muhammu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Babu wata kungiyar data fito tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin. Yau Laraba yan Shiya zasu yi bikin Ashura.