Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Kasar Jamus Na Kafa Sansanin Sojojinta A Nijar Ya Jawo Zazzafar Muhawara


Angela Merkel shugabar kasar Jamus da yanzu take ziyara a Nijar

Shirin Jamus na kafa sansanin sojojinta a birnin Yamai, wai domin ta taimakawa dakarunta wajen 650 dake fafatawa da 'yan tawaye a Mali ya janyo muhawara mai zafi a kasar

Yawancin 'yan kasar ta Nijar na ganin wannan matakin na Jamus da ma wasu kasashen yammacin turai wani yunkuri ne na sabon mulkin mallaka saboda tuntuni Amurka da Faransa suka girke nasu dakarun cikin kasar da sunan yakar ta'adanci..

Wani yace karyar banza ce. Wata hikima ce ta nasara wadda 'yan Afika basu gane ba. Yace sun bari ana ta juyasu yadda su turawan ke so. Yace lokacin da aka yi yakin Biafra a Najeriya ai Faransa bata girke masu sojoji a Nijar ba.

Wani kuma yace menene ake nufi? Ana son ta koma hannun jajayen mutane ne kuma? Su jajayen mutanen su ne zasu dinga bada labari akan kasar, musamman inda duk arzikin kasa yake.

Su ma masana kan harkokin tsaro sun yi tunanen haka. Malam Mamman Sani Adamu masani akan harkokin tsaro yana ganin girke dakarun kasashen turai a kasar tamkar neman mafita ne daga tabarbarewar tattalin arzikinsu ne wanda suka fada ciki. Yace kasashe irinsu Faransa idan suna son su tsira to dole sai sun koma kasashen da suka yiwa mulkin mallaka.

To saidai gwamnatin Nijar na ganin jibge sojojin kasar Jamus a kasar wani cigaba ne na irin dangantakar dake tsakaninsu da ma kasashen yammacin turai..Wai hakan zai samar ma Nijar kayan aiki da samarwa dakarun kasar horo inji Alhaji Yakuba ministan harkokin wajen kasar Nijar.

Ita dai Angela Merkel tana Nijar yau inda ta samu ta gana da shugaba Muhammadou Issoufou.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG