WHO: An Shawo Kan Cutar Polio a Nahiyar Africa

Ana digawa wani yaro maganin Polio

Yankuna biyar daga cikin yankunan Hukumar Lafiya ta Duniya shida da suka hada da nahiyar Afrika, sun shawo kan cutar Polio

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana nahiyar Afrika a matsayin wadda ta shawo kan kwayar cutar Polio. Wannan ya biyo bayan shafe shekaru hudu ba tare da samun wani dauke da kwayar cutar ba.

Da wannan cigaban, biyar daga cikin yankunan WHO shida, da yake kashi casa’in cikin dari na al’ummar duniya, sun huta da wannan cutar da ke gurguntar da mutum. Yanzu kasashen duniya na dab da shawo kan cutar polio. Idan aka cimma wannan burin, zata zama cuta ta biyu da aka shawo kanta bayan ciwon agana.

An dauki shekara da shekaru, ana yaki da cutar,yayinda miliyoyin ma’aikatan jinya suka rika tafiya da kafa, ko cikin kwalekwale, da motocin safa da kekuna domin yiwa kananan yara rigakafin a kauyuka. Ma’aikatan jinyar sun kuma nuna bajinta wajen shiga wuraren da ake fama da tashin hankali domin ceton kananan yara daga cutar da take shanye kafa.

A shekara ta dubu da dari tara da casa’in da tara, shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela, tare da goyon bayan kungiyar Rotary ta kasa da kasa, suka kuduri aniyar shawo kan cutar polio tare da kaddamar da gangamin kawar da cutar Polio a afrika da taken "Kick Polio out Africa". africakicksoutwildpolio.com