Wata Kotun Ingila Ta Bada Belin Jigon Kungiyar WikiLeaks, Julianne Assagne

Hoton masu zanga zanga a harabar wata kotu inda mai kungiyar WikiLeaks ya bayyana yau domin neman beli.

Wata kotun Ingila ta bada belin jigon cibiyar tonon assiran nan ta duniyar gizo mai suna Wkilieaks, watau Julian Assange, amma zai ci gaba da zama kargame.

Wata kotun Ingila ta bada belin jigon cibiyar tonon assiran nan ta duniyar gizo mai suna Wkilieaks, watau Julian Assange, amma zai ci gaba da zama kargame a kurkuku da yake lauyoyin kasar Sweden suna ja da bada belin nasa.

Wani alkali, Howard Riddle ne ya bada belinsda akan $380,000, amma tunda su hukumomin na ja da abin, dole a ci gaba da tsare shi akalla har tsawon sao’i 48 daga yanzu.

Idan za'a iya tunawa cikin makon jiya ne hukumomin Ingila suka tsare Julianne bayan ya mika kansa ga hukumomin kasar.