Wuta: An Shiga Mawuyacin Hali A Jihohin Gabashin Najeriya

Borin da ma’aikatan kamfanin samar da wutan lantarki suka soma a da ya kunshi jihohin Adamawa, Taraba, Borno da Yobe ya soma durkusar da harkokin samar da wutan lantarki, hakan yasa masu karamin karfi ke kira da a shiga tsakani.

Ma’aikatan kamfanin samar da wutar lantarkin a shiyar Yola, ta YEDC, da ke kula da jihohin 4, sun fara ne da gudanar da zanga-zangar lumana na nuna fushinsu tare da zargin cewa mahukuntan kamfanin sun yi burus da wasu bukatun ma’aikatan.

Dalilin da yasa yanzu suka dauki wannan mataki na durkusar da ayyukan samar da wutan lantarkin a wadannan jihohin.

Ma’aikatan dai suka ce, muddun ba’a share musu hawayen su ba, to fa, tabbas zasu cigaba da wannan borin zanga-zangar har illa masha Allah, kamar yadda daya daga cikin shugabanin hadakar kungiyar ma’aikatan samar da wutan lantarkin Kwamared Nasiru Dembo yace, yayi karin baya ni akan abun da yasa su daukan wannan mataki.

To sai dai duk kokarin wakilin muryar Amurka don jin ta bakin babban daraktan kamfanin samar da wutan lantarkin ta YEDC, Engineer Mustapha Ummara, bai yiwu ba.

Amma kuma jami’in hurda da jama’a na kamfanin Mallam Aliyu Ardo, yace wannan yajin aikin idan ya cigaba, zai iya shafar lamurra da dama, kuma yace ma’aikatan sun yi hanzari wajen daukan wannan matakin, amma kuma za’a cigaba da tattaunawa.

A ta bakin jama’a game da halin da aka shiga a yanzu, saboda abin har ya shafi wasu masu karamin karfi.

A Najeriya dai shiga yajin aiki ya zama babban makami wa 'yan kwadago, wajen neman hakkokin su daga gwamnati ko kuma kamfanoni.

Ibrahim Abdul'aziz daha Yola ya hada muna wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Zanga Zangar 'Yan Kamfanin Wutar Lantarki Ya Dakatar Da Aiki A Jihohi 4