Wutar Lantarki Ta Hallaka Wasu Mutane A Gombe

Wayoyin wutar lantarki

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na tsakar dare a lokacin da jama'a ke cikin barci.

Al’ummar da ke zaune a unguwar Tumfure da ke jihar Gombe a arewa maso gabashin Najeriya, sun fuskanci wani ibtila’i cikin dare a lokacin da suke barci, inda babbar wayar wutar lantarki ta zubo akan gidajen mutane.

Kamar yadda bincike ya nuna, hatsarin wutan lantarkin ya faru ne a sanadiyar iska mai karfin gaske wacce ta yi sanadiyyar tsinkiyar wayar wutar daga injin din transforma da ke ba da wuta a wannan yanki na Tumfure.

“Kowane gida ka taba sai wuta ta ja ka, duk wanda ya taba gate ko kofa sai wuta ta ja shi. Akwai da yawa wadanda suka rasa rayukansu.” In ji Jeremiah Galadima Adamu da ke zaune a unguwar ta Tumfure.

Lamarin dai a ya faru ne da misalin karfe 3:30 na tsakar dare.

“Duk wadanda suka rasa ransu, sun je kashe fridge ne ko wani abu, sai wutar ta ja su,” In ji Zainab wacce ke zaune a unguwar.

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammed Inuwa Yahaya ya nuna alhininsa kan wannan al’amari.

“A madadin gwamnati muna masu ba da hakuri, Allah ya ba mu dangana. Alla ya ba mu ikon kiyaye wannan al’amari, muna kuma fatan Allah ya kare na gaba.” In ji Inuwa Yahaya yayin da ya je yin ta’aziyya ga ‘yan uwan wadanda suka rasu.

Alhaji Awwal Baba Jada, shi ne babban jami’in hukumar wutan lantarki da ke lura da shiyyar Gombe, ya kuma tabbara da cewa lamarin ya faru ne sanadiyyar yankewar wayar wutar ta lantarki.

“Babban layi ne ya tsinke ya fado, shi kuma babban layi shi ke dauke da wuta. Mun je mun jajantawa al’umar yankin.”