Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yar Goje Ta Ajiye Aikin Kwamishina A Jihar Gombe


Dr Hussaina Goje (Facebook/ Ma'aikatar Muhalli ta Gombe/ Dan Hassan Photography)

“Ina so na sanar da ku cewa wannan murabus da na yi, na yi shi ne bisa radin kaina. Ina kuma godiya ga gwamna Yahaya da ya ba ni wannan damar ta yin aiki a gwamnatinsa.” In ji Dr Hussaina

Kwamishinar muhalli a jihar Gombe Dr. Hussaina Goje, wacce ‘ya ce ga tsohon gwamna Danjuma Goje ta ajiye aikinta.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, Dr. Goje ta ce ta ajiye aikin ne bisa wasu dalilai na gashin kanta kamar yadda rahotanni suka ce.

Wannan mataki da kwamishinar ta dauka na zuwa ne kasa da sa’a 24 bayan wani hari da aka kai kan ayarin motocin mahaifinta Sanata Danjuma Goje a ranar Juma’a.

Amma Kwamishinar ba ta danganta wannan batu da ajiye aikin da ta yi ba tana mai cewa ta yi ne don radin kanta.

“Ina so na sanar da ku cewa wannan murabus da na yi, na yi shi ne bisa radin kaina. Ina kuma godiya ga gwamna Yahaya da ya ba ni wannan damar ta yi aiki a gwamnatinsa.”

Tsohon gwamna Goje na kan hanyarsa ta shiga garin Gombe daga birnin Abuja a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne, suka far wa ayarin motocinsa.

Amma rahotanni sun ce babu abin da ya same shi.

XS
SM
MD
LG