Ya Kamata EFCC Ta Kama Hadiza Bala Usman – PDP

Hadiza Bala Usman tare da shugaba Buhari (Twitter/ Hadiza Bala Usman)

A farkon watan Mayu shugaba Muhamnmadu Buhari ya dakatar da Bala Usman don a samu damar gudanar da bincike kan zargin da ake mata.

Babbar jami’yyar adawa ta PDP a Najeriya ta nemi a gaggauta hukunta shugabar hukumar da ke kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya ta NPA Hadiza Bala Usman “da aka sallama saboda wawure naira biliyan 165 a hukumar.”

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Kola Ologbondiyan ya fitar, jam’iyyar ta ce ba sallamar ta ya kamata kawai ya kamata a yi ba.

“Ya zama dole a tuhumi Bala Usman kan zargin da ake mata na wawure kudaden da ta yi, kamar yadda ofishin babban mai kididdiga ya gano cewa an sace,” makudan kudade karkashin shugabancinta.

“Jam’iyyar ta PDP na kira ga hukumar EFCC da ta gaggauta kama Bala Usman don ta yi mata tambayoyi kan wadannan zarge-zarge, ciki har da zargin satar naira biliyan 15.18.”

Kazalika jam’iyyar ta nemi EFCC da ta bincike ministan sufuri Rotimi Ameachi wanda a karkashin ma’aikatarsa “aka aikata wannan sata,” a cewar PDP.

“PDP tare da ‘yan Najeriya, za ta ci gaba da sa ido kan al’amuran gwamnatin Buhari sannan ba za ta lamunci duk wani yunkuri da jam’iyyar APC za ta yi na yin rufa-rufa kan wannan al’amari ba.

A farkon watan Mayu shugaba Muhamnmadu Buhari ya dakatar da Bala Usman don a samu damar gudanar da bincike kan zargin da ake mata.

Rahotanni sun ruwatio cewa Bala Usman ta musanta aikata ba daidai ba yayin da take shugabantar hukumar