Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NPA: Buhari Ya Dakatar Da Hadiza Bala Usman, Ya Sa A Bincike Ta


Hadiza Bala Usman tare da shugaba Buhari (Twitter/ Hadiza Bala Usman)
Hadiza Bala Usman tare da shugaba Buhari (Twitter/ Hadiza Bala Usman)

Sai dai wannan sanarwar da fadar ta fitar, ba ta ambaci laifukan da ake zargi ko tuhumar ake yi wa Hadiza Bala Usman da su ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba da umurnin a binciki shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan kasar ta NPA, Hadiza Bala Usman, kamar yadda kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya tabbatar.

Wata sanarwa da Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren Alhamis, ta kuma ce shugaban ya umurci shugabar hukumar ta NPA da ta sauka a mukaminta yayin gudanar da binciken.

“Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shawarar da ma’aikatar sufuri karkashin jagoranci Rotimi Amaechi ta bayar, kan a kafa kwamiti don ya binciki shugabannin hukumar ta NPA.” Sanarawar Garba Shehu ta ce.

“Kwamitin binciken zai samu jagorancin Darektan fannin kula da harkokin sufurin ruwa na ma’aikatar sufurin, yayin da mataimakin darekta na bangaren shari’a zai zama sakatare.”

A cewar Garba Shehu, nan gaba za a nada sauran mamabobin kwamitin binciken.

Sai dai sanarwar ba ta ambaci laifukan da ake zargi ko tuhumar Hadiza Bala Usman da su ba.

Sai dai gabanin kafa kwamitin binciken, rahotanni sun ruwaito cewa an dakatar da ita. Fadar shugaban kasar ta ce an nada Mohammed Koko a matsayin mukaddashin hukumar.

A shekarar 2016 Buhari ya nada Hadiza Bala Usman, a matsayin shugabar hukumar ta NPA.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG