Yadda Biri Ke Girbin Kwakwa a Gonakin Thailand

Yadda Biri Ke Girbin Kwakwa a Gonakin Thailand

“Me ya hada biri da gada,” dadadden karin magana ne a harshen Hausa, wanda akan yi amfani da shi a harkokin yau da kullum, domin kore alaka tsakanin wasu abubuwa biyu.

Amma a dalilin wannan labari mai ban al’ajabi, za mu iya cewa, “me ya hada biri da girbi a gona?

Ma'aikaciyar Muryar Amurka Binta S. Yero ta na shan ruwan kwakwa a gonar

Ma'aikaciyar Muryar Amurka, Binta S. Yero, wacce ta yi tattaki zuwa kasar Thailand a kwanakin baya, ta ziyarci wani tsibirin da ake kira Koh Samui, wanda al’umarsa ke amfani da biri domin cire amfanin gona.

Ba kamar yadda ala’adar noma take a wasu sassan duniya ba, misali, yadda mutane ke girbi da kansu ko kuma su yi amfani da wani nau’in injin domin cire amfani gona, a tsibirin Koh Samui Thailand, wanda Allah ya yalwata da bishiyoyin kwakwa, birrai ne ke girbin kwakwar.

Biri a samar bishiya yana kado kwakwa

Mafi yawan mutane sai sun daura igiya su hau saman itacen su kado kwakwar, sannan su sakko, su sake hawan wani itacen.

“Biri ya fi sauri, shi ba sai ya hau ya kuma sauka akan bishiya ba, zai yi tsalle ne daga wata bishiya zuwa wata, hakan kuma na matukar saukaka mana ayyukanmu.” Inji wani mai kula da wata gonar kwakwa da bai bayyana wa Muryar Amurka sunansa ba.

Akan daura igiya a jikin birin, sai a sake shi ya hau bishiyar - dabarar dauren shi ita ce, a samu damar sa ido akansa, domin kada ya shagala.

Kuma cikin ‘yan dakikoki, zai dane bishiyar, ya tsinko kwakwar ya hurgo ta kasa.

Yadda Biri Ke Girbin Kwakwa a Gonakin Thailand

Dukkanin gonakin da ake noman kwakwa a yankin, da birrai suke amfani wajen yin girbi, sabanin yadda ake amfani da su a sauran sassan duniya.

Ko da yake, kamar yadda bincike ya nuna, akwai wasu a yankin da suke amfani da mutane ko injina wajen girbin kwakwar.

Binciken da ma'aikaciyar Muryar Amurka ta gudanar, ya nuna cewa, akan horar da birran ne a wani wuri, kan yadda za su rika tsinko kwakwar, idan suka kware sai a fara tura su gonaki.

A kasashe da dama, har da wadanda ke nahiyar Afirka, akan ajiye biri ne a gida kawai a matsayin ado ko a kai shi gidan namun daji domin masu ziyara su biya kudi su shiga su yi kallo.

Yadda Biri Ke Girbin Kwakwa a Gonakin Thailand

A wasu lokuta akan yin amfani da shi wajen nishadantarwa. Amma a Koh Samui, tsibirin da ke zaune a can gefen gabashin gabar tekun kasar ta Thailand, birrai abokan harkar noma ne.

“Wannan dadaddiyar al’ada ce ta noman kwakwa da muka jima muna amfani da ita, kuma har ta zama mana jiki ma.” Inji manomi.

Koh Samui, shi ne tsibiri na biyu mafi girma cikin tsibiran da kasar ta Thailand ke da su, wadanda masu yawon shakatawa daga sassan duniya ke kai ziyara.

Bidiyo:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Biri Ke Girbin Kwakwa a Gonakin Thailand