Yadda Matsalar Harbe-Harbe Ta Tsananta a Amurka

Donald Trump ya bukaci a sauke tutocin kasar a gine-ginan gwamnati har na tsawon kwanaki biyar masu zuwa yayin nuna alhini.

A wani mummunan zub da jini na tsawon sa’o’i 13 a Amurka, wasu ‘yan bindiga biyu a wurare daban daban, sun kashe mutum 29 kana suka jikkata wasu da dama, yayin da hukumomi ke ci gaba da binciken musabbabin wadannan munanan hare-hare.

A jiya Lahadi, shugaban Amurka, Donald Trump, ya bukaci a sauke tutocin kasar a gine-ginan gwamnati har na tsawon kwanaki biyar masu zuwa, “yayin nuna alhini da kuma alamar mutunta wadanda mummunan tashin hankalin ya rutsa da su a garin El-Paso na jihar Texas da kuma garin Dayton na jihar Ohio.

Hukumomi sun ce za su nemi a yanke hukuncin kisa ga dan bindigar da ya kai hari a jihar Texas yayin da suke kallon lamarin a matsayin harin ta’addanci na cikin gida.

Shugaba Trump ya fadawa manema labarai a jiya Lahadi cewa, nuna kiyayya "ba shi da muhalli a cikin kasarmu kuma muna aiki tukuru don mu hana faruwar irin wadannan hare-hare nan gaba."

Ya kuma alakanta kashe- kashen da matsalar tabuwar hankali da wasu ke fama da ita.