Yadda Sojojin Nijar Fiye Da 100 Suka Rasa Rayukansu Cikin Wata Daya

Sojojin Kasar Nijar

A cikin wata daya, sojin Nijar sun fuskanci hare-hare da suka hada da na Inates da Samane, da kuma Senegodor, dukkaninsu a cikin yankin Tillaberi, hare haren da suka yi sanadiyyar rasa rayukan sojojin kasar fiye da 100.

Tuni dai ‘yan kasar Nijar suka soma bayyana ra’ayoyinsu game da wannnan alámarin.

Sojojin Kasar Nijar

A harin baya-bayannan da aka kai a Barikin Sojojin Nijar da ke Senegodor gab da iyaka da kasar Mali, wanda ya yi sanadiyyar rayukan sojojin Nijar 25.

A sanarwar da gwamnatin Nijar ta fitar game da wannan harin ta bayyana cewa, sojojin Nijar sun samu goyan bayan takwarorinsu na kasashen waje wanda ya ba su damar halaka ‘yan ta’adda 63.

A cewar Mohamed Abdul Kader shugaban kungiyar fararen hula da ake kira Gyara Kayanka, al’ummar Nijar za ta ga tasirin sojojin kasahen waje.

Sai dai a nasa bangare, Idi Abdu, daya daga cikin masu fashin bakin al’umran yau da kullum a Nijar ya bayyana cewa, lokaci ya yi da shugabannin kasashen G 5 Sahel ya kamata su dogara da dakarun kasashensu maimakon dogara da na kasashen waje.

Sojojin Kasar Nijar

Shi kuma a nasa bangare, Dauda Tankama, mataimakin shugaban kungiyar fararen hula CADDED ya bayyana cewa, dole Nijar ta nemi gudunmuwar kasashen waje a wannan yaki.

A ranar13 ga wannan wata na Janairu shuwagannin kasashen na G 5 Sahel zasu gudanar da wani taro tsakaninsu da shugaban kasar Faransa a birnin Pau kan batun Sojojin Faransa dake Nijar.

A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Yusuf Abdoulaye a birnin Yamai.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Sojojin Nijar Fiye Da 100 Suka Rasa Rayukansu Cikin Wata Daya