Yajin Aikin Ma’aikatan Majalisun Najeriya Ya Shiga Rana Ta Hudu

Yajin aikin kungiyar ma'aikatan majalisun dokokin Najeriya.

Yau aka shiga rana ta huku da kasancewar zauruka da harabobin majalisun dokokin jihohin Najeriya 36 a garkame, biyo bayan yajin aikin da kungiyar ma’aikatan majalisun ke yi, akan batun aiwatar da dokar tabbatar da ‘yancin gashin kai ta fuskar kudade da ma’aikata.

Gabanin tsunduma wannan yajin aiki na sai baba ya gani, sai da shugabancin kungiyar na kasa baki daya ya yi gargadin makonni uku a karon farko kana ya kara makamancin sa na tsawon makonni biyu.

A hirar sa da Muryar Amurka, Comrade Ubale Yusuf, shugaban kungiyar ma’aikatan majalisun dokokin Najeriya reshen jihar Kano ya bayyana cewa, za su ci gaba da rufe majalisun har zuwa lokacin da za a samu daidaito bisa ga umarnin da su ka samu daga shugabannin kungiyar na kasa.

Yajin aikin kungiyar ma'aikatan majalisun dokokin Najeriya

Shi kuwa takwaransa na jihar Jigawa, comrade Umar Adamu Kazaure cewa yake yajin baya nufin kassara ayyukan majalisar dokoki a jihohi. Bisa ga cewarsa, sun shiga yajin aikin ne domin karfafa aikin majalisa. Yace aikin majalisar shine, kafa doka, idan kuma za a kafa doka a samu wani bangare a kasar yana keta dokar ya nuna ke nan ana yi wa aikin majalisar zagon kasa.

Karin bayani akan: Jihar Kano, majalisun dokokin najeriya​, Nigeria, da Najeriya.

Yanzu haka dai kungiyoyin rajin shugabanci na gari a Najeriya sun fara tsokaci akan wannan batu.

Da yake tsokaci kan lamarin, Comrade Abdulrazak Alkali guda cikin ‘yan gwagwarmayar shugabanci na gari a Najeriya ya bayyana cewa, ba alfarma wani zai yi wa majalisun ba, amma doka ce ta tsara a basu kudaden gudanar da ayyukansu kai tsaye daga matakin tarayya.

Hatimin ikon alkali

Bisa ga cewarsa, kungiyarsu ta tunkari majalisun jihohi da dama inda suka shawarcesu su tabbatar sun ci moriyar wannan doka da shugaban kasa ya jadada cewa lallai a gudanar da wannan dokar.

A nasa banagaren, Sanata Mas’udu Eljibril Doguwa wakili a majalisar dattawan Najeriya ya bayyana cewa, rashin aiki da duk wata dokar kasa abin kyama ne.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Yajin Aikin Ma’aikatan Majalisun Najeriya Ya Shiga Rana Ta Hudu-3:30"