'Yan Adawar Hong Kong Sun Yi Zaben Fidda Gwani Na 'Yan Rajin Dimokradiyya

Kusan mutum 600,000 suka kada kuri’unsu a wani zaben fidda gwani da aka yi ba tare da amincewar hukumomin Hong Kong ba, domin tantance shugabannin masu rajin kare dimokradiyyar da za su tsaya takara a watan Satumba.

Bangaren ‘yan adawa a yankin na Hong Kong ne ya shirya wannan zabe, wanda ake gani ya saba wa sabuwar dokar nan mai cike da takaddama da hukumomin Beijing suka kafa a yankin.

A dai watan Satumba ake shirin yin zaben ‘yan majalisar dokoki a Hong Kong.

Daruruwan dubban mutane ne suka fita wannan zabe a karshen makon da ya gabata, duk da cewa hukumomi sun yi gargadin hakan zai saba wa sabuwar dokar tsaro da China ta saka wa yankin.