Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Kun San Adadin Masu Coronavirus a Duniya?


Adadin Masu Coronavirus a Duniya
Adadin Masu Coronavirus a Duniya

Adadin wadanda cutar COVID-19 ke kamawa a duniya na ci gaba da karuwa a kullum yayin da Amurka ke ci gaba da zama kasar da ta fi kowacce yawan masu cutar a duniya.

Annobar coronavirus ta cimma wani sabon matsayi, inda adadadin wadanda aka tabbatar sun kamu cutar ya haura miliyan 12, a cewar jami’ar Johns Hopkins da ke kididdiga kan cutar.

Amurka ce take kan gaba a jerin kasashen duniya da adadi mafi yawa da suka kamu da COVID-19 wanda ya kai 3,054,695, wato kashi hudu na adadin wadanda suka kamu da cutar a duniya, ciki har da sabbin mutum dubu 60,000 da cutar ta harba a ranar Laraba, wanda shi ne adadi mafi yawa a rana daya tun lokaci da ta cutar barke.

Akalla jahohi biyar na Amurka da suka hada da California, Texas, Tennessee, West Virginia da Utah sun bayyana adadi mafi yawa na sabbin wadanda suka kamu a ranar Laraba.

Hakan na faruwa ne yayin da jihohi da dama suka samu sabbin wadanda suka kamu cikin kwanaki bakwai.

Jami’an lafiya a jihohin Arizona, California, Florida da kuma Texas sun yi gargadin cewa shashen kula da marasa lafiya na gaggawa a jihohin na su sun kusa cika ko sun ma cika.

Amurka ita ce take kan gaba na wadanda suka mutu na COVID-19, inda take da mutum 132,500, kusan kashi daya bisa hudu na mutane 550,600 da suka mutu a duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG